Ƙabilun Sudan Ta Kudu na gwabza yaƙi
November 17, 2011Wasu daga cikin ƙabilun Sudan Ta Kudu dake gwabza yaƙi a tsakanin su dai su ne na Loguri da Yondu, waɗanda ke taƙaddama akan wani yankin da bai taka karya ya karya ba kusa da Iyakar Sudan Ta Kudu da ƙasar Yuganda. Babu abinda mutum zai gani idan ya ziyarci yankin da ake tada jijiyar wuya akan sa illa ciyayi da hanya maras kyau dake janyo matsala ga manyan motoci ɗaukar kaya, sakamakon daminar da ta sauko. Sai kuma wasu gidajen lakar da aka lalaata saboda tashe-tashen hankulan da ƙabilun biyu ke yi akan mallakar fili. Pastino Lokujakia Ambo, wani tsoho ne- ɗan ƙabilar Yondu, ya ce abin taƙaici ne halin da suka samu kansu a ciki:
" Ya ce ƙabilun Loguri da Yondu sun ɗauki tsawon lokaci suna faɗa da juna. An yi kissar jama'a ta hanyar amfani da kwari da baka, inda wasu kuma suka sami rauni. Al'ummar Loguri ta ɗauki makamai da ta yi amfani da shi wajen harbe wasu 'yan Yondu, tare da ƙona wasu daga cikin gidajen su. Mun kai ƙarar su zuwa ga kwamishinan 'yan Sandan yankin, amma babu wani matakin daya ɗauka."
Gabannin shekara ta 2002 dai, al'ummomin Loguri da Yondu suna zaman lafiya a yankin, kafin daga baya 'yan ƙabilar Loguri suka fara yin barazanar fatattakar ƙabilar Yondu daga yankin. Sai dai kuma babu wanda zai iya tantance ainihin ƙabilar da ke da gaskiya game da taƙaddamar, amma rigingimu bisa haƙƙin mallakar filaye sun zama ruwan dare tun bayan yaƙin basasar daya kawo ƙarshe a shekara ta 2005. Abin farin ciki dai, shi ne an sami wata ƙungiyar da ta ƙware wajen warware rigingimu a yankin. Peter Tibi, shi ne babban darektan ƙungiyar, wadda ake kira da suna " RECONCILE"
" Ya ce a lokacin yaƙi, mutane da dama ko dai sun rasa matsugunan su ko kuma sun tsere daga Sudan zuwa wasu ƙasashen Afirka. To, yanzu da aka sami zaman lafiya, sai suka dawo kuma yawan mutane ya riɓanya na da. Kowane Iyali na son mallakar ƙasar Noma da gida, abinda kuma ya janyo taƙaddama akan mallakar filaye."
Buƙatar warware rigingimu a tsakanin ƙabilun yankin
Alamu dai na nuna cewar, gwamnatin Sudan Ta Kudu ba tada sukunin tinkarar irin waɗannan matsalolin. Rundunar tsaron ƙasar ta ƙunshi tsoffin 'yan tawaye ne da ba su da horon da ake buƙata da kuma kayayyakin aiki. A cewar Pter Tibi, baya ga haka ma akwai wani dalilin da ke ruruta rikici a Sudan Ta Kudu:
" Y ace, har yanzu akwai makamai a hannun fararen hula. Ka san idan ana yin rikici, mutane na yin amfani da bindigogi ne, kuma idan da za'a ƙwace bindigogi daga ko dai manoma ko kuma makiyaya ne, to, kuwa da za mu samu zaman lafiya a cikin al'umma, ba tare makamai ba."
A yanzu dai ƙungiyar "Reconcile" da Peter Tibi ke wa jagoranci ta fara shiga tsakani domin warware rikicin dake tsakanin ƙabilun Loguri da kuma Yondu, domin hana shi yaɗuwa. Sai dai ana ci gaba da samun rigingimu a wasu yankunan ƙudancin Sudan, ba tare ɗaukar matakan shawo kan su ba.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Ahmad Tijani Lawal