Ƙungiyar AU ta gargaɗi Sudan da Sudan ta Kudu da su tattauna
December 15, 2012Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka ta yi kiran da a gaggauta sake koma kan tebrin shawarwari tsakanin Sudan da Sudan ta kudu,akan taƙddamar da suke yi akan yanki nan mai arzikin man fetir na Abyei da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Tattaunawa da nufin samun sulhu tsakanin sasan biyu ita ce za ta tantance makomar yankin wanda har yanzu bai san tudun dafawa ba.Wani kwamitin tsaro na ƙungiyar da ke shiga tsakanin ƙasashen biyu wanda suka dakatar da yaƙi a watannin da suka gabata, ya bai wa hukumomin Khartum da na Juba wa'adin ranar biyar ga wannan wata na su sasanta sai dai, lokacin har ya zo ya wucce ba tare da a ɗimke ɓarakar. Ƙungiyar ta haɗin kan ƙasashen Afirka ta yi gargaɗin cewar akan rashin ɗasawa da aka gaza cimma tsakanin ƙasashen biyu to kam su zasu ɗauki mataki.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh