Kungiyar IS ta ƙwace birnin Al-Walid
May 24, 2015Talla
Mayaƙan ƙungiyar 'yan Jihadi ta IS sun ƙwace birnin Al-Walid da ke kan iyakar da ta raba ƙasashen Siriya da Iraƙi a ranar Lahadin, bayan da sojojin tsaron kan iyakar ƙasashen biyu suka fice daga garin ba tare da sun yi wata fafatawa.
Shi dai wannan birni na Al-Walid na a matsayin wani guri inda sojin kasar ta Iraƙi masu samun dafawar mayaƙan ƙungiyoyin 'yan Shi'a ke ƙoƙarin yin amfani da shi domin ƙaddamar da harin neman kwato birnin Ramadi wanda ya faɗa a hannun mayaƙan Ƙungiyar ta IS .Kama wanan birni dai , ya wakana kwanaki ukku bayan da dama mayaƙan Ƙungiyar ta IS suka ƙwace yankinsa da ke a cikin ƙasar Siriya na Al-Tanaf.