Ƙungiyar Taliban ta kai hare-hare a Pakistan
June 9, 2014Talla
Rundunar sojojin ƙasar Pakistan ta ba da sanarwar cewar ta sake ƙwace iko da filin saukar jiragen sama na Karachi. Bayan da wasu 'yan bindigar ɗauke da manyan makamai suka mamaye filin saukar jiragen sama na birnin wanda ke ɗaya daga cikin manyan filayen saukar jiragen sama na ƙasar.
Sojojin sun ce murƙushe maharan bayan da aka kwashe tsawon sao'i shida ana shan gumurzu inda wuta ta turniƙe sararin samaniya. Wani kakakin rundunar sojojin ƙasar ya ce mutane a aƙalla 28 suka mutu haɗe da 'yan bindigar da kuma sojojin gwamnatin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman