2015 a cikin hotuna: Afirka na fafutukar dimokaradiyya
Shugabannin kasashe da ke son dawwama a kan karagar mulki da al'ummar kasar da basu amince ba. Fafutukar tabbatar da dimokaradiyya da bijirewa, sun kasance abin da ya faru a 2015 a Afirka. Waiwaye cikin hotuna.
"Ba mu amince da tazarce a karo na uku ba"
Dubban mutane sun fito kan tituna a Burundi bayan da shugaban kasar ya ayyana yin tazarce a karo na uku. Kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa shugaban kasa damar yin mulki karo biyu, sai dai an gyara kundin a watan Yuli inda Shugaba Pierre Nkurunziza ya samu damar yin tazarce a karo na uku. Jami'an tsaro na cin zarafin masu zanga-zanga da ma kashesu. Kasar na cikin hadarin fadawa yakin basasa.
Cece-kuce da makwabciyarta Ruwanda
Rikicin kasar Burundi ya taba dangantakar da ke tsakaninta da makwabciyarta Ruwanda. Shugaba Paul Kagame (a hagu) ya soki lamirin Nkurunziza (a tsakiya) da cewa: yana kashe al'ummarsa. Sai dai shi ma Kagame ba ya son sauka daga mulki. Tsarin mulkin kasarsa bai ba shi damar tsayawa takara a 2017 ba, sai dai yana son ya sauya shi. Al'ummar Ruwanda sun kada kuri'ar raba gardama a kai.
Kongo-Brazzaville: Shekaru 30 a kan karagar mulki ba su wadatar ba
Shi ma Denis Sassou-Nguesso na son yin tazarce. Shekarunsa 72 a duniya, shekaru sama da 30 yana mulki a Kongo-Brazzaville. Yayin kuri'ar raba gardama kan yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar a watan Oktoban da ya gabata, an samu hargitsi. Sakamakon zaben ya nuna yardar al'umma, 'yan adawa sun ce an tafka magudi. A makwabciyarta Kongo al'ummar kasar na zanga-zanga kan tazarcen Joseph Kabila.
Canjin gwamnati mai tarihi a Najeriya
A Najeriya Muhammadu Buhari ya zama shugaba a watan Maris, shi ne dai karo na farko da aka mika mulki daga jam'iyya mai mulki zuwa wata. Ba wanda ya tsammaci wanda ya gada Goodluck Jonathan zai mika mulki cikin ruwan sanyi. Buhari na son kawo karshen cin hanci da ake fama da shi a bangarorin gwamnati da dama. Ya bayyana kadarorinsa. Babban kalubalensa shi ne: Yaki da Boko Haram.
Ba wani sauyi: A Habasha gwamnati na da kaso
A karshen watan Mayu al'ummar Habasha kimanin miliyan 35 sun zabi sabuwar majalisar dokoki. Sakamakon zaben ya nunar da cewa jam'iyyar da ke mulki ta 'Ethiopian People's Revolutionary Democratic Front' ta lashe kujeru 547. Jam'iyyar adawa da ke da wakili guda a majalisar ta kaurace wa zaben. Gwamnati ta takura wa 'yan adawa da 'yan jarida gabanin zaben, abin da ya samu suka daga masu sanya idanu.
Tanzaniya: Me Magufuli zai cimma?
#WhatWouldMagufuliDo#: A karkashin wannan alamar, ra'ayin jama'a ya yadu ta hanyar amfani da Twitter. Sabon shugaban kasar Tanzaniya John Pombe Magufuli ya ce zai samar da sababbin gadaje masu tsada a asibitoci. Ba kowa ne ke murna ba. 'Yan adawa sun yi zargin magudin zabe, inda suka ce su suka samu nasara kana ba su amince da Magufuli ba. Masu sanya idanu sun tsammaci nasarar 'yan adawa.
Côte d'Ivoire: 'Ado' na da goyon bayan mata
Cikin fargaba al'ummar Côte d'Ivoire suka tunkari zaben 25 ga watan Oktoba, ganin yadda zaben shugaban kasar da ya gudana a shekaru biyar din da suka gabata ya janyo yakin basasa. A wannan karon cikin ruwan sanyi Alassane Ouattara mai lakabin: Ado ya lashe zaben. Mariame Souaré (a hagu) ta yaba masa tun a yakin neman zabe. Ouattara na magana da magoya bayansa musamman mata a yakin neman zabe.
Angola: Tuhumar masu fafutuka
Matasan Angola sun yi zanga-zanga a gaban kotu a babban birnin kasar Luanda. A ciki ana gudanar da shari'ar masu fafutuka na kungiyar matasa 17. Sun hadu a wani shagon sayar da littattafai domin yin zanga-zangar lumana. An zarge su da shirya juyin mulki. José Eduardo dos Santos shi ne shugaban kasar Angola tsawon shekaru 36, yana murkushe masu yin suka ga gwamnatinsa.
Mali ba ta samu nutsuwa ba
A tsakiyar watan Mayu gwamnatin Mali ta yi sulhu da kungiyoyin tawayen kasar masu yawa. Cikin watan Yuni 'yan tawayen Abzinawa sun sanya hannu. Bayan tsawon lokaci ana tattaunawa, ta yiwu a samu zaman lafiya a Arewacin Mali. A watan Agusta Abzinawa sun sake kai hari. A watan Nuwamba 'yan ta'adda sun yi garkuwa da mutane 170 a wani Otel a Bamako babban birnin kasar. Mutane 20 ne suka mutu.
Jajircewa a Burkina Faso
Samun nasara a zagayen farko mai ban mamaki: A karshen watan Nuwamba al'ummar Burkina Faso sun zabi Roch Marc Christian Kaboré a matsayin sabon shugaban kasa, shekara guda bayan da aka tilasta wa Shugaba Blaise Compaoré da ya kwashe tsawon sherau 27 ya a mulki sauka daga mukaminsa. An tsara gudanar da zaben a watan Oktoba amma juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Satumba ya tilasta daga zaben.
Hargitsi da yaki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Ya kamata su ma al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya su gudanar da zabe a watan Oktoba. Yawan tashe-tashen hankula a kan tituna tsakanin Musulmi 'yan tawayen Séléka da kuma tsagerun Kiristoci na Anti-Balaka, ya hana ruwa gudu. An sanya karshen watan Disamba a matsayin sabon lokacin gudanar da zabukan. A 'yan kwanakin nan al'ummar kasar sun amince da sabon kundin tsarin mulki a zaben raba gardama.