Mabiya addinin Kirista na gudanar bikin Kirsimeti
December 25, 2024Talla
Tun daga jiya Talata da maraice ne dai aka fara shagulgula na bikin inda Paparoma Francis da ke jagorantar mabiya darikar Katolika ya jagoranci mabiyansa wajen yin ibada a majami'ar nan ta St. Peters Basilica da ke Vatican.
Nan gaba a yau ne kuma Paparoman zai yi jawabinsa na al'ada da ya saba yi a irin wannan rana ga mabiya addinin na Kirista, inda ake sa ran jawabin zai mayar da hankali kan rikicin da ake yi a yankin gabas ta tsakiya da kuma yakin da Rasha ke yi a kasar Ukraine.