Abba Kyari, jigo a gwamnatin Shugaba Buhari ya rasu
April 18, 2020Babban jami'i mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ne ya sanar da wannan labarin a shafinsa na twitter a tsakar daren da ya gabata. Marigayi Malam Abba Kyari, wanda dan saba'una ne, ya kwanta jinyar cutar ta COIVD-19 ne a Legas kafin Allah Ya yi masa wa'adi, bayan komawa kasar daga Jamus da ma ziyarar da ya kai kasar Masar.
Fadar shugaban na Najeriya ta bayyana kaduwarta da rashin jami'in da ake ganin wani mai fada a ji ne daga cikin mukarraban Muhammadu Buhari a gwamnatin kasar. Malam Abba Kyari wanda da make da wasu matsaloli na lafiya, shi ne dai babban jami'i na farko da ya rasa ransa sanadin wannan annoba a nahiyar Afirka baki daya.
Cutar ta Corona ta kashe mutum 17 ke nan a Najeriyar, yayin da wasu 493 ke jinyarta.