Shirin ya yi nazari nazari kan halin da mata da ke zuwa aikatau kasar Saudiyya daga kasashen Afirka musamman Najeriya da Nijar ke tsintar kansu. A kwai dai tarin kalubale, kama daga matsalar bautarwa da azabtarwa kai har ma da cin zarafi ta hanyar fyade.