Salon rayuwa
Abu Namu: 'Yancin mata a kasashen Larabawa
MNA
March 9, 2020Talla
A kowacce ranar takwas ga watan Maris ake gudanar da bikin ranar mata ta duniya, da nufin bayyana 'yancin da matan ke da su da kuma yakar abubuwan da suka danganci take musu hakkokin nasu. Taken bikin na bana shi ne: "Daidaita 'Yanci ga Kowa". Dangane da hakan, shirin na wannan lokaci zai yi nazari kan batun 'yancin mata a wasu kasashen Larabawa inda za mu isa kasar Saudiyya domin jin yadda Yarima mai jiran gado, Muhammad Bin Salman ke ci gaba da daukar matakan kyale matan kasar su sakata su wala, sabanin a baya da matan kasar da ma duniya baki daya ke ganin 'yancin mata a Saudiyya na cikin wani wadi na tsaka mai wuya.