SiyasaGabas ta Tsakiya
Mutane 27,131 suka halaka a yankin Zirin Gaza
February 2, 2024Talla
A wannan Jumma'a ma'aikatar lafiya ta yankin Zirin Gaza ta Falasdinu ta fitar da sabbin alkaluma na kimanin mutane dubu-27 suka halaka yayin da wasu kimanin dubu-66 suka jikata.
Ita dai Isra'ila ta kaddamar da farmaki kan yankin bayan hare-hare da tsagerun kungiyar Hamas da galibin manyan kasashen suka dauka a matsayin 'yan ta'adda suka kai hare-haren kan Isra'ila da halaka fiye da mutane dubu-daya da 200.