AEC: Za a yi sabon zama kan kasar Burundi
July 3, 2015Talla
Kamar sauran da suka gudana na baya a ranakun 13 da kuma na 31 ga watan Mayu da ya gabata, shi ma wannan taron na shugabannin kasashen Gabashin na Afirka zai gudana ne a birnin Dar Es-Salaam na kasar Tanzaniya, inda shugabannin za su yi bitar halin da ake ciki kan rikicin kasar Burundi tun bayan tarurukansu na baya.
Kasashen dai sun hada da kasar ta Burundi, Tanzaniya, Ruwanda, Yuganda da kuma Kenya wadanda kamar sauran kasashen duniya da ma manyan kungiyoyi irin su Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka, ke neman a dage zabukan kasar ta Burundi ya zuwa 30 ga watan nan na Yuli.