Afganistan: IS ta kai hari ofishin "Save the Children"
January 24, 2018Talla
Maharan sun dana manyan rokoki a cikin motar da suka tarwatsa a harabar ofishin. Rahotannin hukumomi tsaro na cewa jami'ai sun yi yunkurin katse harin bayan da aka gano maharan na sanye da kakin soja.
Wannan sabon hari ya zo ne kwanaki kalilan bayan wani hari da ake zargin kungiyar Taliban ta kai wani Otel da ke Kabul babban birnin kasar, inda aka samu asarar rayukan mutane 22 yawanci 'yan kasashen waje.
A yanzu dai wannan sabon hari ya tilastawa kungiyar Save the Children mai cibiya a Birtaniya daukar matakin dakatar da kuma katse dukkannin ayyukanta a fadin kasar Afganistan.