1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afganistan: An kai hari cibiyar hukumomin tsaro

Abdul-raheem Hassan
January 21, 2019

Wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa bam da ke cikin mota dauke da ababen fashewa, yayin da wasu maharan suka shiga ofishin hukumar leken asirin Maidan Shahr babban birnin lardin Wardak da ke tsakiyar Afganistan.

https://p.dw.com/p/3BuIw
Afghanistan Explosionen und Schüsse am Parlament in Kabul
Hoto: Reuters/M. Ismail

Rahotanni daga Afghanistan sun ce fiye da mutane 100 suka halaka a cibiyar horas da jami'an tsaro, yayin da wasu da dama suka jikkata. Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin, amma hukumomi sun tabbatar da mutuwar dukkanin maharan.

A baya-bayan nan mayakan Taliban na zafafa kai hare-hare kan jami'an tsaro da hukumomin gwamnatin Afganistan, amma dakarun kawance da Amirka ke jagoranta na ikirarin nasara a cigaba da kaddamar da samame da suke yi kan sansanonin mayakan.