An yi Allah wadai da Jami'an hukumar zabe a Afghanistan
October 21, 2018Talla
Shugaban hukumar zaben Abdul Baddi Sayyad ya bayyana cewar sama da mutane milyan 3 ne suka kada kuri'unsu a ranar Asabar din da ta gabata kafin 'yan ta'adda su kai hari a wasu mazabun a fadin kasar, lamarin da ya kassara zaben.
Don haka ne hukumar ta fara aikin tattara sakamako daga mazabu 253 wadanda yamutsin na jiya bai hada da su ba daga nan sai ya bayyana takaicinsa game da jami'an hukumar da suka yi jinkirin fitowa kan lokaci lamarin da janyo jama'a suka fara korafi.
Sama da mutane 28 sun rasa ransu yayin da wasu 102 suke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali sakamakon mummunan harin da 'yan ta'adda suka kai wasu mazabun yayin da jama'a ke tsaka da kada kuri'u a jiya Asabar.