Afghanistan: Taliban ta kashe 'yan sanda
October 30, 2017Talla
Jami'ai a kasar Afghanistan, sun ce wasu mayakan Taliban sun kaddamar da wani hari da ya halaka 'yan sanda tara a gabashin lardin Ghazni. A cewar mai magana da yawun gwamnan lardin, Arif Noori, akwai wasu 'yan sanda hudu da suka jikkata aharin na wannan Litinin.
Jami'in ya kuma ce jami'an tsaron, sun yi nasarar kashe 'yan Taliban din su bakwai tare da raunata wasu, a musayar harbe-harbe na sa'a guda da ta wakana tsakanin bangarorin biyu. Ko da yammacin wannan Lahadi ma dai mayakan na Taliban, sun afkawa wani shingen jami'an tsaro dake lardin Zabul inda aka rasa 'yan sanda akalla shida.