1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
August 21, 2020

Juyin mulki da sojoji suka yi wannan mako a kasar Mali ya dauki hankalin jaridun Jamus a labarai da kuma sharhin da suka kan nahiyarmu ta Afirka.

https://p.dw.com/p/3hHsF
Mali Militär
Sojoji sun yi nasarar hambarar da gamnatin Ibrahim Boubacar Keita na MaliHoto: AFP

Jaridar Die Tageszeitung ta fara da cewa sojoji a Mali sun hambarar da zababben shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita. Ta ce sojojin da wasunsu suka samu horo daga sojojin Jamus da ke aiki a Mali, sun cimma abin da bore da zanga-zangar fararen hula suka kasa. Jaridar ta ce abin da ya faro da safiyar ranar Talata a barikin Kati a matsayin boren nuna rashin gamsuwar sojoji, kafin yamma ya rikide zuwa juyin mulkin soja a wannan kasa da ke kan gaba wajen samun taimakon kayan aikin soja da horo daga ketare.

Murabus din dole

Bisa la'akari da wannan ana iya cewa horon da aka ba su ya yi nasara, domin masu juyin mulkin sun samu horo mai kyau da kuma kayan aiki. Bayan murabus da aka tilasta wa Shugaba IBK yi, sojojin sun ce sun dauki matakin ne domin ceto kasar daga fadawa karin matsaloli, sannan sun yi alkawarin gudanar da zabe na gaskiya da adalci a wani lokaci nan gaba. Sai dai juyin mulki a wannan zamani abin yin kaico ne ba kuma abin karbuwa ba ne, musamman a kasa irin Mali wadda wani juyin mulkin soji a shekarun baya ya share fage ga kungiyoyin masu da'awar jihadi da suka yi ta cin karensu babu babbaka.

Karikatur Mali Krise
Murna ko fargaba?Hoto: DW/A. Baba Aminu

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhin da ta yi kan juyin mulkin na Mali cewa ta yi, abubuwan da ke faruwa yanzu na yin tuni da rikicin Malin ta tsunduma ciki shekaru takwas da suka gabata, lokacin da wani gungun sojoji karkashin jagorancin Amadou Sanogo suka hambarar da shugaban kasa Amadou Toumani Touré. Daga barikin sojan na Kati boren juyin mulkin na shekarar 2012 ya samo asali.

Ci-gaban mai hakan rijiya?

A lokacin Sanogo ya ce rashin horo da ya dace ga sojoji da kuma cin hanci da rashawa suka sa ya yi juyin mulkin, amma kuma ba a jima ba sai ilahirn yankunan kasar in ban da birnin Bamako, suka fada hannun 'yan tarzoma. Girke sojojin duniya ya sa lamura suka yi dan sauki. Shi ya sa a wannan karo ma idan ba a yi da gaske ba, masu ikirarin Jihadi ka iya yin amfani da halin da ake ciki na rashin tabbas don fadada aikace-aikacensu, domin da ma ba wai an ci galaba a kansu ba ne.

Sudan Karthoum | Proteste gegen die Übergangsregierung
Ba ta sauya zane ba a SudanHoto: picture-alliance/AA/M. Hjaj

Daga juyin mulkin kasar Mali sai wani sabon boren a kasar Sudan, a cewar jaridar Die Tageszeitung Zeitung. Ta ce dubun-dubatar mutane sun sake gudanar da zanga-zanga a Khartoum babban birnin kasar Sudan albarkacin cika shekara guda da amincewa da yarjejeniyar nan ta tarihi ta ranar 17 ga watan Agustan 2019, bayan boren juyin-juya hali da ya yi awon gaba da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasa Omar al-Bashir a shekarar ta 2019. Jaridar ta ce masu zanga-zangar sun nuna rashin gamsuwa da yadda sababbin mahukuntan na Sudan da ke cikin gwamnatin wucin gadi ta sjoji da farar hula ke tafiyar da kasar tsawon shekara guda. Talakawa dai na korafin cewa fatan da suka yi na samun ingantuwar rayuwa sakamakon nasarar juyin juya halin, har yanzu bai tabbata a zahiri ba. Kamar a lokacin mulkin kama karya, a wannan karon ma 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zangar.