1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka

Suleiman Babayo AH
December 31, 2021

Batun rasuwar Desmond Tutu wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka jagoranci gwagwarmayar yaki da gwamnatin wariyar launin, da rikicin siyasar Mali da kuma na Sudan sune suka dauki hankali a Jaridun na Jamus.

https://p.dw.com/p/451jU
Südafrika Kapstadt Trauer um Desmond Tutu
Hoto: AP/picture alliance

 Jaridar Frankfurter  Allegmein Zeitung ta yi sharhi kan rayuwar Marigayi Desmond Tutu wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka jagoranci gwagwarmayar yaki da gwamnatin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu. Jaridar ta yi tuni da lokacin da mutane kimanin 50,000 suka hallara a filin wasa na birnin Johannesburg a watan Afrilun shekara ta 2010, gabanin kasar ta dauki nauyin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, inda daukacin filin wasan ya dauki sunan "Tutu" daga kowanne bangare a wani bikin mawaka da aka shirya. Shi dai Marigayi Desmond Tutu a matsayin mai wa'azi na addinin Kirista ya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata, kuma ya yi fice a Afirka kan kare hakkin dan Adam. Haka ita ma jaridar Berlin Zeitung ta mayar da hankali kan rasuwar Marigayi Desmond Tutu wanda ya bar duniya yana da shekaru 90 da haihuwa, wanda Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya bayyana a matsayin mai tasiri ga rauwar kasa kuma marigayin ya kasance murya wadda take nuna abin da ya kamata ga rayuwar kasa baki daya. Marigayi Desmond Tutu da Marigayi Nelson Mandela tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu sun kasance mutanen da suke da matukar tasiri a rayuwar mutanen Afirka ta Kudu.

Mali na fuskantar rikici mafi girma tun lokacin data samun 'yanci kai a 1960

Putschistenführer Assimi Goita in Mali als Staatschef vereidigt
Hoto: Habib Kouyate/XinHua/dpa/picture alliance

Jaridar Züddeutsche Zeitung ta yi sharhi kan kasar Mali, da ke cewa kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka tana fuskantar rikici mafi girma tun da kasar ta samu 'yanci a shekarar 1960. Sojojin sun kwace madafun ikon kasar abin da ya janyo mayar da kasar saniyar ware tsakanin kasashen duniya, lokacin da take tsakiyar matsalolin masu tayar da kayar baya da sunan jihadi, ga yunwa, ga talauci da suka yi wa kasar katutu. Kan haka jaridar ta yi hira da Oumar Yamadou Diallo masanin tarihi kana tsohon daraktan gidan kula da kayan tarihi na kasar wanda ya ce kasar ta kasance mai tunkaho da al'adunta da nuna sanin ya kamata. Amma yanzu duk suna cikin mawuyacin hali.

Manyan hafsoshin sojin Sudan sun sake dawo kan adafun iko

Sudan Khartoum | Proteste | Demonstranten
Hoto: AFP/Getty Images

Ita ma jaridar Die Zeit ta mayar da hankali kan kasar Sudan inda ta ce manyan habsoshin soja na kasar sun sake dawowa kan madafun iko. Yayin da matasa ke ci gaba da gwagwarmayar neman ganin an tabbatar da tsarin dimukaradiyya, tun bayan juyin-juya halin shekara ta 2019. Fiye da mutane 45 sun halaka tun watan Oktoba sannan wasu daruruwa sun jikata sakamakon kai ruwa rana tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaron kasar ta Sudan.