1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu tanadin yaki da Corona a Afirka

Zainab Mohammed Abubakar ZU
March 20, 2020

Jaridun sun dubi shirin da nahiyar Afirka ta yi wa manyan cututtuka irinsu Corona da Ebola da kuma batun biyan bashin da Chadi ta yi wa Angola da dabbobi a maimakon kudi.

https://p.dw.com/p/3Znrq
Südafrika Kapstadt | Coronavirus | Busbahnhof
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Jaridar Die Zeit ta wallafa mai taken "har yanzu mutane kalilan ne suka kamu da Corona a Afirka, sai dai nahiyar bata yi wa annobar tanadi ba, bisa la'akari da barnar da annnobar Ebola ta yi" .

Jaridar ta ci gaba da cewar an ga yadda jami'an kiwon lafiya a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo suka yi ta bukukuwa bayan sallamar mara lafiya na karshe da ya warke daga cutar Ebola a 'yan makonnin da suka gabata ba tare da sanya kayan kariya ba.

Kasar ta Kongo dai ta yi fama da Ebola mafi tsanani a tarihinta cikin shekara guda da rabin da ya gabata, cikin wani yanayin da za a iya kwatantawa da wadda kasashe masu ci gaba na duniya suka tsinci kansu a yau saboda annobar Corona.

Daga cikin mutane 3,444 da suka kamu dai 2,264 sun rasa rayukansu. Akwai sama da yara kananan 500 da ke cikin jerin mutanen da suka rasa rayukansu.

Tsakanin shekarun 2014-2016 sama da mutane dubu 11,000 suka rasa rayukansu daga Ebola, akasari a yammacin Afirka da cutar ta fi barna. Duk da cewar Ebola ta fi hadari, hanyar kamuwa da Corona ta iska take kuma tana yaduwa cikin sauki, sabanin Ebolar da sai ka taba ruwan da ya fita daga jikin wanda ke da ita.  Akan haka ne ake dasa ayar tambaya ko shin kasashen Afirka sun shiryawa wannan annoba?

Yadda wasu jama'a suka rinka gudu ke nan don tsira daga annobar guguwar Idai a kasar Mozambik a 2019
Hoto: Reuters/S. Sibeko

 

 

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi, yankin gabashin Afirka bai tsira daga cutar Corona ba. Shekara guda ke nan da yankin ya fuskanci mummunar guguwar Idai.

Guguwar da ta yi illa a kasashen Mozambik da Malawi da Zimbabuwe. Sama da mutane 1,300 suka rasa rayukansu ta hanyar ambaliyar ruwa ko faduwar gini akansu da kuma cutar Kwalera, daura da dubban daruruwan wasu da suka rasa muhallinsu. Bankin duniya ya kiyasta cewar, an yi asarar kwatankwacin dalar Amirka biliyan biyu.

Duk da cewar wasu mutane sun koma matsugunnensu, akwai akalla sama da 93,000 da ke ci gaba da rayuwa cikin tantuna. Mutane miliyan 1.6 a Mozambik kadai na rayuwa kan tallafin da Majalisar Dinkin Duniya ke bayarwa, daura da yara 30,000 da ke fama da karancin abinci mai gina jiki.

Shugaban Kasar Chadi Idriss Deby
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

 

Daga batun annobar Corona da bala'in guguwa, bari mu karkata zuwa harkar kasuwancin shanu, inda jaridar ddeutsche Zeitung ta rubuta wani sharhi mai taken " Salon kasuwanci da ba a saba gani ba tsakanin Chadi da Angola".

Ba dai abu mai sauki ba ne jigilar shanu 1000 daga kasar Chadi zuwa tashar jiragen ruta da ke Angola. Abin da aka saba gani a wannan tashar dai tankuna danyan mai ne, amma a wannan karon sai ga shanu ana saukewa.

Chadi dai bata da teku, don haka sai da aka yi jigilar shanun zuwa Najeriya, kafin aka turasu cikin jirgin ruwa zuwa Angolar.

Kafofin yada labarun Angolan dai sun yi murnar isar shanun cikin koshin lafiya, kasancewar wannan shi ne rukuni na farko, wasu shanun na hanya. Shanun na a matsayin biyan bashin dalar Amirka miliyan 100 ne da gwamnatin Chadin ta karba daga wajen Angola a 2017.

Ga kasashen biyu dai wannan hanyar ita ce mafita. Chadi mai yawan al'umma miliyan 14, bata da kudin da za ta mayar da rancen, amma tana da shanu wajen miliyan guda. Cikin shekaru goma, Angola za ta karbi shanu kimanin dubu 75 daga wajen Chadin.