Corona ta haifar da tarnaki a bukukuwan aure a Afirka
December 15, 2020Yanayin da aka saba bukukuwa a kasashen Afirka sun sauya salo a wannan shekara ta 2020. Matakai kamar sanya tazara tsakanin mutane da karayar tattalin arziki sun jefa amare da angwayensu cikin wani mawuyacin hali.
Bisa ga al'ada dai aure ba karamin buki ba ne ga 'yan Afirka, wuri ne da iyalai da 'yan uwa da abokan arziki na ango da amarya kan hadu cikin farin ciki, ana ci ana sha, a wasu lokutan da raye-raye. A kan dauki tsawon watanni ana shirin wannan babbar rana, ba tare da la'akari da matsayin masu auren ba.
Najeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da suka kafa dokar takaita yawan mahalarta buki zuwa mutum 50 a watan Mayu saboda karuwar yawan masu kamuwa da cutar corona.
Sai dai ga Adebayo Denis Ojo da ke shirin aure, takaita yawan masu zuwa bukinsa ba zabi ba ne.
"Ina shirin yin bukina lokacin da corona ta bayyana, mun rigaya mun sayi wasu abubuwan buki kamar shinkafa. Covid-19 ta kawo hauhawar farashin komai. Na sa 28 ga watan Disamba a matsayin sabuwar ranar buki. Matsalar kawai ita ce yanzu komai ya sauya, farashin buhun shinkafa ya hau, ba a maganar irinsu tumatiri."
A Najeriyar dai iyalan ango ne ke da alhakin biyan sadaki ga bangaren na amarya. Ya kan zo a matsayin kudi ko kuma kadara, ko duka biyu, kuma iya kudinka iya shagalinka. A daya bangaren kuma uban amarya shi ne ke da alhakin sayen kayan gidan ga sabbin ma'auratan a cewar wani uba Kabiru Sani daga Najeriya.
"Bisa ga al'adarmu ta kaka da kakanni, uba ne ke daukar nauyin idan batun aure ya taso, sai dai Covid-19 ta janyo karayar tattalin arziki kasancewar iyayen masu shirin auren ba sa iya samar da dukkan abubuwan da ake bukata a al'adance, da suka hadar da gado, kujeru har zuwa kayan girki. Abin da wuya sosai, kasancewar annobar ta janyo tsadar rayuwa a bangaren mu iyaye".
A kenya masu daukar nauyin shirya buki kamar Wanjira Kago ta bayyana cewar harkoki sun tsaya cik saboda illar Covid-19.
"Lamarin bai zo mana da sauki ba, kasancewa duk mun dage bukukuwan da ke gabanmu, wasu ma sun soke auren. Wannan ita ce rayuwarmu a yanzu. Fatanmu kawai shi ne rayuwa za ta inganta. 'Yan kasuwa da yawa sun tsayar da harkokinsu. Wasu masu sayar da abinci, yanzu sai kaiwa suke daga ofis zuwa ofis."
Duk da cewar gwamnatoci da dama sun dage wadannan dokoki na takaita yaduwar corona, amma har yanzu farashin kayan abinci na kara hawa a yawancin kasashe kamar Najeriya da Kenya, kuma tsadar abinci na nufin tsadar kusan komai. Sai dai fa al'adar Afirka al'ada ce da duk rintsi duk wuya sai an kwatanta ta.