Shari'a kan zargin da ake wa Zuma
July 19, 2021Talla
Ana wannan zaman kotu ne ta kafar bidiyo, sai dai lauyan da ke kare tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya nemi a dage zaman, domin ya samu damar halartar kotun a nan gaba. Duka wannan na zuwa ne bayan da Zuma ya kwashe sama da mako guda a gidan yari bisa laifin raina kotu da ya yi, lamarin da ya janyo gagarumar tarzoma a kasar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200 da jikkata wasu da dama, baya ga kone gine-ginen gwamnati da na al'umma gami da wasoson dukiya.