1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ANC na kan gaba a zaben Afirka ta Kudu

May 9, 2019

Kamar yadda hasashe ya nunar kafin gudanar da zaben, akwai yiyuwar jam'iyyar ANC mai mulki ta yi nasara a babban zaben na ranar Laraba.

https://p.dw.com/p/3IFj2
Südafrika - Wahl / Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: picture-alliance/B. Curtis

Sakamakon farko na zaben 'yan majalisun dokoki da na larduna a kasar Afirka ta Kudu na nuni da cewa jam'iyyar African National Congress, ANC, mai mulki ce ke kan gaba da kashi 56 cikin 100 na kuri'un da aka kada, jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance, DA, na biye da kashi 23.4 yayin da jam'iyyar Economic Freedom Fighters, EFF ke mataki na uku da kashi 9.3. Amma rahotanni na cewa akwai yiyuwar alkaluman su sauya ganin har yanzu ba a kai ga kidayar rabin kuri'un da jama'a suka kada ba.

Fulufhelo Nelwamondo, masani ne a kasar ta Afrika ta Kudu, da ya ce sai jam'iyyar ta ANC yi da kyar kafin ta kai ga samun nasara don kuwa da bambanci a tsakanin zaben na bana da na shekarar 2014 da ta sami rinjaye.

''Shakka babu mun yi hasashen akwai yiyuwar ANC ta sami nasara, muna kallon ta sami tsakanin kashi 56 zuwa 57 cikin 100 na akasarin kuri'un da aka kada.''

Südafrika, Partei der Demokratischen Allianz startet Wahlprogramm
Shugaban jam'iyyar Democratic Alliance, Mmusi Maimane da jam'iyyarsa ke matsayi na biyuHoto: Reuters/S. Sibeko

Jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance dai ta fuskanci koma baya duk da cewa ita ke biye da jam'iyyar ta ANC, yayin da ita kuma jam'iyyar Economic Freedom Fighters ta iya ba da mamaki.

Pule Mabe shi ne mai magana da yawun jam'iyyar ta ANC.

''Muna samun kwarin gwiwa da alkaluman da ke shigowa duk da cewa wani hanzari ba gudu ba, ba ma batun yin shelar nasara a wannan lokacin.''

Masana dai sun baiyana damuwa kan karancin masu zabe, sun ce babu mazabar da aka sami kashi 70 cikin 100 na masu kada kuri'a, sabanin yadda lamarin ya kasance a zaben 2015. Masanan sun danganta rashin fitowar jama'a da matsaloli na rashin abubuwan more rayuwa da cin hanci da suka yi wa kasar katutu.

Susan Booysen, ita ce darekta ta wata kungiyar mai aikin bincike a fagen siyasa ta yi tsokaci tana mai cewa.

''Alkaluma sun nuna kasa da kashi 70 cikin 100 ne suka fito don yin zabe zai yi wuya ya ma kai kashi 65 cikin 100 na wanda suka yi zaben.''

Südafrika EFF Wahlkampfauftakt 2019 Julius Malema
Julius Malema lokacin yakin neman zaben jam'iyyarsa ta EFF a birnin PretoriaHoto: Getty Images/AFP/P. Magakoe

Hukumar zaben kasar wato IEC ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin da wasu ke yi na cewa akwai wadanda suka yi zaben har sau biyu, a dalilin rashin ingancin tawadar da hukumar ta tanadar. An gano cewa tawadar na saurin wankewa abin da ya sa wasu suka yi ta dangwala wa jam'iyyun da suka fi so fiye da sau guda.

Mosotho Moepya, jam'in hukumar ne ga abin da yake cewa.

"Tsarin ya kunshi tantance takardar rajistar zabe, in kuma mutum zai yi zaben a wata mazaba dabam wadda ba a nan ya yi rajista ba dole ya gabatar da takardar rantsuwa da ya karbo daga kotu kafin ya sami izinin gudanar da zabe.''

Hukumar dai ta ce komai ya tafi daidai duk da cewa akwai wasu mutum hudu da ake tsare da su bisa laifi na magudin zabe, ta kuma ce a ranar Asabar mai zuwa za a sanar da sakamaon zaben gaba dayansa.