Afirka ta Kudu: Tsugune ba ta kare ba
July 15, 2021Jami'an 'yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 6 yayin da dama suka jikkata, kana jami'an suka kame mutum fiye da dari 2 dake da suke zargin da hannunsu a tada tarzomar. Rahotanni na nuna cewa masu zanga-zanga a kasar sun fasa kantuna tare da dibe kayayyakin dake ciki. Tuni dai aka rufe kantuna da bankuna da gidajen mai da sauran mahimman wurare a wasu biranen kasar.
Rikicin dai ya samo asali ne biyo bayan karar da kotun tsarin mulkin kasar ta shigar na sake nazari kan hukuncin zaman gida yari da ta yankewa Zuma bisa laifin raina kotu da yayi. A ranar 29 ga watan Junin da ya gabata ne dai kotu a kasar ta yankewa shugaba Zuma hukuncin zaman gidan kaso na watanni 15 saboda watsi da bincike kan cin hanci da rashawa da ake zargin an tafka a lokacin mulkinsa.