1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ina aka kwana a amfani da kudin Eco?

Eric Topona AMA/LMJ
July 2, 2020

A Larabar wannan makon, daya ga watan Yulin da mu ke ciki ne ya kamata a fara amfani da takardar kudin bai daya ta "Eco" a wasu kasashe takwas renon Faransa da ke yankin yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/3edsj
Westafrika CFA-Franc BEAC
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wannan takardar kudin dai an shirya za ta maye gurbin takardar kudin CEFA da kasashen Afirka rainon Faransa ke amfani da ita tsawon shekaru 46 da suka gabata. A yayin wani babban taron kolin da kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, wato ECOWAS ko CEDEAO da ya gudana a ranar 29 ga watan Yunin shekara ta 2019 da ta gabata ne dai, daukacin kasashe mambobin kungiyar suka amince da soma amfani da takardar kudin ta bai daya mai suna "Eco". To sai dai ba zato ba tsammani batun na yukurin samar da takardar kudin bai dayan, ya soma ficewa daga hannun yankin na yammacin Afirka zuwa wasu kasashen mambobin kungiyar UEMOA da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.

Shisshigi daga Faransa?

A cikin watan Disambar baran ne dai, Shugaba Alassane Ouattara na Côte d'Ivoire da takwaransa Emmanuel Macron na Faransa, suka bayyana fara amfani da kudin na Eco a Abdijan fadar gwamnatin Ouattara, a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS ke kaddamar da babban taronta, inda za ta tattauna a kan batutuwa ciki har da na kudin Eco. Wannan lamari ya haifar da diga wata babbar ayar tambaya kan abin da yake faruwa a tsakanin kasashen na rainon Faransa da takwarorinsu da ke yammacin Afrikan, wanda har ta kai ga sun shiga mamaki da rudanin matakin da Faransa wacce ta yi wa mafiya rinjayen kasashen yankin da ke cikin kungiyar ta CEDEAO mulkin mallaka ta dauka.
To ina aka kwana game da batun takardar kudin na bai daya na takardar Eco? Thierno Thioune, malami ne a tsangayar kula da tattalin arziki da jagoranci a jami'ar Cheick Anta Diop da ke Dakar babban birnin kasar Senigal: "Har yanzu ina cikin tababa duba da yadda kasashen ke fama da matsalar annobar coronavirus da ta kawo illa kan tattalin arzikin kasashen. To amma ina da yakinin cewa har yanzu kasasshen ba za su cimma matsayar da aka gindaya ta muradin samar da kudin na bai daya ba, wanda idan aka lura da hakan za a iya cewa akwai wuya takardar kudin ta soma aiki a wannan Larabar daya ga watan Yulin na 2020."

Nigeria Abuja | ECOWAS-Treffen
Taron ECOWAS ko CEDEAO a AbujaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Najeriya na jan kafa

Kasashe da dama dai sun nuna dari-dari game da batun kudin na Eco musamman ma Tarayyar Najeriya da ke zama uwa ma ba da mama a fannin tattalin arzikin kasashen yankin, lamarin da wasu masu sharhi ke ganin na da hannu wajen kawo tarnaki ga tarkardar kudin bai dayan mai suna Eco. Hatta ma Thierno Thioune na jami'ar ta birnin Dakar na da yakin cewa Najeriya na da wata muhimmiyar rawar takawa idan har ta so, ta hanyar shiga a dama da ita a tsarin kudin na Eco, ba tare da samun wani nakasu ba. Ga alama dai sanarwar ta tsakiyar watan Disambar 2019 da shugabannin kasashen Cote d'ivoire da Faransa suka bayar ta kawo karshen kudin CEFA tare da maye gurbinsa da kudin Eco, na iya zama wani abu mai kamar wuya ko kuwa gidan tsunstu kawai ba tsuntsun, inji masana a fannin tattalin arziki. A yanzu dai kallo ya koma kan yadda za ta kaya game da samar da kudin na bai daya, walau na Econ da Faransa ta ke jagoranta ko kuwa na kasashen yankin yammacin Afirka ciki har da Najeriya, wacce ita ce ke zaman kashin bayan tattalin arzikin yankin kuma ke ci gaba da nuna turjiya har sai ta ga abin da ya fitarwa tulu gashi.