Afonso (I)- Ya shiga cinikin bayi
April 15, 2021A yaushe ne Sarki Afonso I ya rayu?
An haifi Sarki Afonso I na Kwango, a shekara ta 1456, ya gaji mahaifinsa Sarki João I na Kwango, ya kuma mulki masarautar tsakanin shekara ta 1507 zuwa 1542.
Da me Sarki Afonso I ya yi kaurin suna?
A lokacin da mahaifinsa ya karbi baki matafiya daga kasar Portugal, shi Sarki Afonso ya koma addinin kirista inda ya yi watsi da addinin gargajiya. Wasu masana tarihi na ra'ayin cewa wata dabara ce da kulla alaka da Turawan. Sai dai ya mayar da hankali ne ga samun amfani daga Turawan, kamar yadda ya fito cikin wasu wasikun da ya rubuta wa Sarki Manuel I na kasar Portugal, musamman a lokacin da harkar cinikin bayi ta dagule.
Me matsayin ilimi ga Sarki Afonso I?
Addini kirista ya shiga kasar Kwango ne da tsarin karatu da rubutu kuma a matsayinsa na shugaba, Sarki Afonso ya ci gaba da musayar wasiku a tsakaninsa da Sarkin kasar Portugal. Galibin wasikun kuma sun shafi addini ne na kiristanci da kuma tsari na gudanarwa. Ya kuma aika daya daga cikin ‘ya'yansa, Henrique Kinu na Mvemba, domin samun horo a matsayin babban limamin Katholika. A karshe kuwa Henrique ya zama kusan abin da ake iya cewa Bishop na farko dan Afirka bakar fata a shekarar 1518.
Yaya aka yi Sarki Afonso ya shiga harkar cinikin bayi?
Mutane da dama sun soki tsoma hannu da Sarki Afonso ya yi a harkar cinikin bayi. Cinikin bayin dai a wancan zamani ba laifi ba ne domin ko da a kasashen Afirka ma ana samun hakan, wato wadanda ake mayar da su bayi daga cikin fursunonin yaki. Sai dai dillancinsu ya bambanta da wadanda ake fitar da su da jiragen ruwa, saboda ana kallonsu kamar sauran mutane masu ‘yanci; kai a wasu lokutan ma suna sake sama wa kansu ‘yanci su kuma ci gaba da rayuwa. Masarautar Portugal na daukar su bayin a matsayin wata haja mai daraja. Kuma Sarki Afonso ya shiga addinin kirista da niyyar samun damar cefanar da bayin ne ba tare da masaniyar matsalolin da ke cikin musayar da za ta wakana da masarautar Portugal ba, wacce za ta taimaka mata wajen kafa gwamnati da kuma kawo sabon addini ga al'umar wancan zamani.
Ko Sarki Afonso ya yi dogon nazari kan cinikin bayin?
A lokacin da aka kafa gonaki masu yawa a São Tomé, bukatar leburori ta kama karuwa, kuma jin kadan bayan nan, harkar bayin ta dagule. Sarki Afonso ya kama rubuce-rubucen wasiku ga Sarki Manuel I na kasar Portugal, cewar wannan tsari na rage masa yawan al'uma sannu a hankali ya kuma so a kawo karshensa. "Kasarmu na ganin raguwa daga al'umarta fiye da kima, kuma Mai Martaba ba zai amince da hakan ba na sani'' a cewarsa. Ya kammala da fadin hakan "ba za mu lamunta da dorewarsa ba a masarautunmu, saboda haka babu batun cinikin bayi ko ma wata hanya ta fitar da su."
Wannan ciniki dai ya kafu ne saboda hadamar fataken da suka fito daga Portugal da ma bangaren mutanen Sarki Afonso wadanda ya ce suna da matukar bukatar kayayyakin da suke fitowa daga ‘yan Portugal da ke hada-hada a yankin a wancan zamani.
Wannan makalar ta samu ne tare da tallafin shawarwarin kimiyya daga masana tarihi irin su Farfesa Doulaye Konaté da Dakta Lily Mafela, Ph.D. da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo. Tushen Afirka dai shiri ne da gidauniyar Gerda Henkel ta dauki nauyinsa.