Afrika 2019: Ebola da Juyin juya hali
Fama da annobar Ebola a Kwango, Firaministan Habasha ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel, ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a Gabashin Afirka. Waiwaye na abubuwan da suka faru a Afirka a 2019 cikin hotuna.
Felix Tshisekedi ya zama shugaban Kwango
A farkon shekarar Felix Tshisekedi ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Jamhuriyar Demukuradiyyar Kwango. An yi takaddama kan sakamakon zaben. Tshisekedi ya yi alkawarin sauye-sauye da yakar 'yan tawayen kasar. Bayan shekara guda fatan ganin canji ya dushe: ana yi wa Tshisekedi kallon dan koran tsohon Shugaba Joseph Kabila, wanda ya mulki kasar tsawon shekaru18.
Wa'adin mulki na biyu ga Shugaban Najeriya
A Najeriya shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya lashe zabe da yawan kuri'u fiye da miliyan uku. Buhari ya ba da muhimmanci kan batutuwan yaki da talauci da rashin tsaro. Wannan na da matukar muhimmanci domin har yanzu arewacin kasar na fama da rikicin mayakan Boko Haram. Rikici tsakanin makiyaya da manoma shi ma ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, hatta ma a kasashen Mali da Nijar.
Guguwar Idai da Kenneth
Masifofin guguwa masu karfi guda biyu sun farma gabashin Afirka a shekarar ta 2019. A watannin Maris da Afrilu guguwar sun yi kaca-kaca da wasu yankuna a kasashen Madagaskar, Mozambik, Zimbabuwe, Malawi, Tansaniya da kuma tsibiran Komoro. Fiye da mutane 1400 suka rasu,da yawa sun bata. Dubun dubatan mutane sun rasa ginshikin rayuwarsu. Kwalera ta barke a gaba dayan yankin da guguwar ta shafa.
Juyin juya hali a Sudan
'Yar kasar Sudan Alaa Salah ta zama alamar juyin juya halin: hauhawar farashin kayan abinci da tabarbarewar tattalin arziki su ne sanadiyyar boren a fadin kasar. A cikin watan Afrilu sojoji sun kifar da Shugaba Omar Al-Baschir bayan kusan shekaru 30 yana mulki. An kafa gwamnatin riko tsakanin sojoji da farar hula. Mutane da yawa sun mutu sakamakon juyin juya halin.
Wasan cin kofin kwallon kafa na Afirka
Kungiyar kwallon kafa ta kasar Madagaskar ta ba da mamaki a gasar cin kofin kwallon kafar Afirka. Ta yi wa Najeriya da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango fintinkau, ta yi gwagwarmaya har zuwa "kwata final". A karawar karshe (hoto) Aljeriya ta yi nasara kan Senegal. Da farko an shirya yin gasar a kasar Kamaru, amma aka mayar zuwa Masar saboda rikicin siyasar Kamaru.
Annobar cutar Ebola ta girgiza Kwango
Tun a watan Agustan 2018 Jamhuriyar Demukuradiyyar Kwango ke fama da annobar cutar Ebola: A jimilce fiye da mutane 3300 suka kamu da kwayar cuta, kashi biyu cikin uku suka rasu. A tsakiyar Nuwamba Yuganda ta tabbatar da karshen annobar Ebola a lardin Kasese a kan iyaka da Kwango. Wata allurar riga kafi ta yi nasara kan kwayar cutar, haka ma wasu magunguna da aka yi amfani da su kan masu cutar.
Abiy Ahmed ya ci kyautar zaman lafiya ta Nobel
Firaministan Habasha ya cimma yarjejeniyar zaman lafiya da makociyar kasa Eritiriya bayan shekaru gommai na yaki tsakaninsu. Saboda haka ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel. Abiy ya samu nasarar daidaita lamura a kasarsa mai kabilu 80 da kuma ke fama da rarrabuwar kai, ya saki dubban firsinonin siyasa. Ya aiwatar da canje-canjen tattalin arziki ya kuma saka mata a majalisar ministocinsa.
Takaddama game da zabukan kasar Mozambik
Shugaba Filipe Nyusi ya lashe zaben da gagarumin rinjaye. Jam'iyyar adawa ta yi watsi da sakamakon zabe ta kuma zargi Nyusi da jam'iyyarsa da tabka magudin zabe. Jam'iyyun guda biyu sun gwabza mummunan yakin basasa har zuwa shekarar 1992. Kusan mutane miliyan daya suka rasu sakamakon yakin. A watan Agusta sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, sai dai har yanzu ana zaman dar-dar a kasar.
Murnar samun sabuwar jiha a Habasha
A watan Nuwamba kashi 98,5 cikin 100 na mazauna yankin Sidama sun kada kuri'ar amincewa da sabuwar jiha da kuma karin 'yancin cin gashin kai. 'Yan Sidama, na biyar mafi girma a kabilun Habasha, na fatan samun iko da albarkatun karkashin kasa da fada a ji a siyasar kasar da kare al'adunsu da kuma karfafa su. Wasu karin kabilu 10 sun nuna sha'awar gudanar da irin wannan kuri'ar raba gardama.
Zaben shugaban kasa zagaye na a Guinea-Bissau
Tun a zagaye na farko shugaba mai ci Jose Mario Vaz ya sha kaye. A ranar 29 ga watan Disamba aka gudanar da zagaye na biyu na zaben tsakanin Domingos Simões Pereira da Umaro Sissoco Embaló. Takaddama da aka dade ana yi tsakanin Shugaba Vaz da majalisar dokoki ta janyo rugujewar hukumomin gwamnati da matsalolin tattalin arziki. Dole ne sabon shugaban kasa ya warware takaddamar.
Hare-hare kan Majalisar Dinkin Duniya a Kwango
A karshen watan Nuwamba masu zanga-zanga a birnin Beni da ke gabashin Jamhuriyar Demukuradiyyar Kwango sun farma wani sansanin Majalisar Dinkin Duniya, sun kuma cinna wa ofishin magajin gari wuta. Sun zagi sojojin MDD da rashin ba su kariya daga hare-haren 'yan tawaye. Sojojin sa kai na kungiyar ADF sun halaka gommai na mutane sun kuma yi garkuwa da wasu a yankin, ana ci gaba da fada a Beni.
Zanga-zanga a Zimbabuwe
A Zimbabuwe shekarar ta fara ta kuma kare da bore. Hauhawar farashi ta ninka da kashi 400, dubban mutane sun fantsama kan tituna suna zanga-zanga, kayan abinci sun yi karanci a shaguna. An kori likitoci 211 daga cikin 1550 da ke aiki a asibitocin gwamnatin kasar saboda sun yi zanga-zangar neman a inganta yanayin aiki. Suka ce ba za su iya rayuwa da albashi na kasa da dala 200 a wata ba.