Gabas ta Tsakiya: Bukatar agajin Chaina
October 14, 2023Kiran sakataren harkokin kasashen wajen Amurkan Antony Blinken na zuwa ne sakamakon shiga cikin halin dar-dar na fargabar hare-haren ramuwar gayya, biyo bayan harin ba-zata da kungiyar Hamas da ke gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza na Falasdinu ta kai kan Isra'ila. Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen wajen Amurkan Matthew Miller ne ya sanar da hakan, inda ya ce Blinken ya yi wannan kiran ne yayin ziyarar da yake a Saudiyya a tattaunawar sa'a guda da ya yi da takwaransa na Chainan Wang Yi ta wayar tarho. A cewarsa Blinken na fatan rikicin ba zai bazu ba, kuma ya bukaci Chainan ne da ta sanya hannu ganin irin dangantakarta da Iran da shugabannin addinin kasar ke goyon bayan Hamas da sauran kungiyoyin da ke da ikon fada a ji a yankin Zirin Gaza na Falasdinun.