Agajin gaggawa ga Sudan ta Kudu
February 4, 2014Talla
Majalisar ta ce da waɗannan kuɗaɗe za ta taimaka wa mutane kusan miliyan uku waɗanda yaƙin da ake fama da shi tun a tsakiar watan Disamba shekara bara ya tagayara.
Da ya ke yin magana shugaban agajin jin ƙai na MDD a Sudan ta Kudun Toby Lanzer. Ya ce abu na farko da zasu yi da kuɗaɗen shi ne ceton rayuka da abinci da magunguna da kuna sauran kayayyaki na buƙata, ta yadda ƙungiyoyin agaji zasu iya kaiwa ga jama'a da ke a cikin ƙauyuka kafin saukar damina lokacin da hanyoyin mota ke lalacewa. MDD ta ce faɗan ya tilastawa mutane kusan dubu ɗari tara barin gidajensu kana wasu dubu goma suka mutu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh