AKK: ''Ba zan nemi shugabancin gwamnati ba''
February 10, 2020Talla
To sai dai Kramp-Karrenbauer ko kuma AKK kamar yadda ake kiranta ta ce sai za ta cigaba da kasancewa a matasayinta na ministar tsaro kana shugabar jam'iyyar CDU har sai an fidda sabon shugaban jam'iyyar.
Da dama dai na alakanta wannan matsayin da ta dauka da irin rashin samun goyon bayan jiga-jigan jam'iyyar ta CDU da kuma irin gazawar da ta yi wajen jan hankalin 'yan jam'iyyarta na kaucewa bada goyon bayansu wajen fidda shugaban gwamnati a jihar Thunrigia, inda aka kafa gwamnati tare da ban hannun 'yan jam'iyyar nan ta AfD da ke kyamar baki.