1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamun ci-gaba a tattaunawa tsakanin Amirka da Taliban

Mohammad Nasiru Awal AS
February 12, 2020

Tun a shekarar 2018 bangarorin biyu ke zaman tattaunawa a Doha duk da fadan da ke ci gaba a fadin Afghanistan, lamarin da ya yi sanadi na asarar rayukan daruruwan farar hula da sojoji.

https://p.dw.com/p/3XfKq
Afghanistan | Friedensgespräche mit Taliban
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Qatar Ministry of Foreign Affairs

Wasu majiyoyin gwamnatin Afghanistan da na jami'an diflomasiyyar kasashen yamma sun ce akwai yiwuwar sanya hannu kan wani shirin zaman lafiya tsakanin Amirka da kungiyar Taliban a wannan wata idan har Taliban din ta rage yawan hare-hare, abin da kuma zai kai ga janyewar dakarun Amirka daga Afghanistan.

Wannan labarin daga majiyoyin ya zo ne kwana guda bayan da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya ce akwai alamun an samu gagarumin ci-gaba a tataunawar da ake yi tsakanin Amirka da wakilan Taliban a kasar Qatar.

Tattaunawar dai ta cije a wasu bangarorin musamman dangane da bukatar Amirka cewa dole sai masu tada kayar bayan su amince su rage yawan tada zaune tsaye a matsayin wani bangare na yarjejeniyar janye dakarun Amirka daga Afghanistan.

Suhail Shaheen da ke zama kakakin ofishin kula da lamuran siyasa na Taliban a birnin Doha na kasar Qatar ya ce tabbas an samu ci-gaba amma ya ki yin karin bayani.

Tun a shekara ta 2018 bangarorin biyu ke zaman tattaunawa a Doha duk da fadan da ke ci gaba a fadin kasar Afghanistan, lamarin da ya yi sanadi naasarar rayukan daruruwan farar hula da sojoji.