Akwai barazana ga makomar demokraɗiyya a Senegal
February 3, 2012A dai halin da ake ciki yanzu gasar ƙwallon ƙafa ta ci kofin Afirka ta shiga mataki na biyu, inda ƙasashen Gabon da Equatorial Guinea dake karɓar baƙuncin gasar suka samu kafar tsallakewa zuwa wannan mataki. Amma fa babbar abokiyar burmin cinikin ƙasar Gabon, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta nunar, ba abin da ta sa gaba in banda maslaharta ta tattalin arziƙi a ƙasar. Abin nufi a nan kuwa ita ce China, wadda aka ce ta taimaka wa Gabon da tsabar kuɗi dala miliyan ɗari bakwai da hamsin wajen gina hanyoyin sadarwa dangane da gasar ta cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afirka.
A can ƙasar Senegal, wadda a cikin tarihi aka santa da zaman lafiya da kwanciyar hankali, ana fama da zanga-zangar adawa da shugaba Abdullaye Wade, dake fafutukar yin ta zarce bayan wa'adin mulki sau biyu da daftarin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar. Akan haka jaridar Süddeutsche Zeitung ke cewa:
"A halin yanzu haka murna na neman komawa ciki dangane da al'amuran ƙasar Senegal, wadda ita ce ƙasa ɗaya ƙwal a yammacin Afirka da ba ta taɓa fuskantar juyin mulkin soja ba. Zanga-zangar adawa dake addabar ƙasar tayi sanadiyyar rayuka kuma 'yan adawa sun ce ba zasu dadara ba har sai sun ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Kuma ƙiyawa ƙememe da shugaba Abdullaye Wade mai shekaru tamanin da biyar na haifuwa yake yi na ci gaba da mulki ba alheri ba ne ga makomar ƙasar. Senegal dai ƙasa ce da mulkin demokraɗiyya ya kankama a cikinta kuma akasarin al'umar ƙasa ba zasu yarda wani da ba ya hangen nesa yayi wa tsarin nasu ƙafar ungulu ba."
Akwai alamar cewa 'yan tsagera na ƙabilar Hutu dake da shelkwatarsu a dajin kurmin gabashin Kongo na fuskantar barazanar wargajewa. Ana wa manyan kwamandojin ƙungiyar FDLR ta 'yan tsageran Hutun Ruwanda kashe-kashe na gilla kuma dakarunta na cin karensu babu babbaka a cewar jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta ƙara da bayani tana mai cewar:
"A baya ga matsalar ta yi wa kwamandojin kisan gilla, akwai kuma matsalar guzuri. Domin kuwa kawo yanzu ƙungiyar na samun taimako ne daga daga 'yan ƙasar Kongo sakamakon kyakkyawar alaƙar dake tsakaninsu. Amma a yanzu wannan dangantakar ta gurɓace kuma ana fuskantar barazanar yunwa a yankin da ƙungiyar ta girka shelkwatarta. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasce cewar yawan mayaƙan ƙungiyar FDLR a yanzun bai zarce dakaru dubu biyu kacal ba daga dakaru dubu ashirin a zamanin baya."
Da yawa daga ƙwararrun masana na hasashen kyakkyawar makoma ga nahiyar Afirka, inda suka ce mai yiwuwa nahiyar ta maye gurbin ƙasashen Asiya wajen samun bunƙasar tattalin arziƙi. Amma fa akwai matsaloli da dama da ya wajaba a shawo kansu tukuna. Daga cikin matsalolin kuwa har da alaƙar tattalin arziƙi da kasuwanci tsakanin su kansu ƙasashen Afirkan, wanda a shekara ta 2010 bai zarce kashi goma sha biyu cikin ɗari na hada-hadar cinikin ƙetare na ƙasashen nahiyar baki ɗaya ba, kamar yadda jaridar Handelsblatt ta rawaito.
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi