1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai yiwuwar aikewa da sojojin ketare a Ukraine

December 18, 2024

Taron kasashen Turai da za a yi a Beljiyam a wannan Laraba, zai dubi bukatar kai sojojin kiyaye zaman lafiya a Ukraine wadda Rasha ta afka wa da yaki tun cikin watan Fabrairun 2022.

https://p.dw.com/p/4oHiV
Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine
Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine Hoto: Virginia Mayo/AP Photo/picture alliance

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce akwai yiwuwar tattaunawa kan batun aikewa da dakarun kiyaye zaman lafiya na ketare a kasarsa, a taron da za a yi a yau Laraba a tsakaninsa da shugabannin kasashen Turai a birnin Brussels da ke a Beljiyam.

Taron da zai dubi yadda za a taimaka wa Ukraine din tun kusan shekaru uku da Rasha ta kaddamar yaki wurjanjan a kanta, zai samu halartar shugabannin Jamus da Faransa da Poland da ma na kungiyar kawancen tsaro ta kasashen yammacin duniya wato NATO.

Da ma dai shugaban na Ukraine, ya fito ya bayyana lokacin wata ziyarar da ya kawo nan Jamus a ranar 9 ga wannan wata, wannan batu na dakarun kiyaye zaman lafiya a kasar tasa.

Yiwuwar samun hakan har ila yau, batu ne da shugaban Faransa Emmanuel ya fada cikin watan Fabrairu, sai dai shugabannin kasashen Turan ba su amince da shi ba.