Al-Bashir ya ce Trump na da saukin kai
November 30, 2016Talla
Shugaba Omar Hassan al-Bashir na kasar Sudan da kotun hukunta masu manyan laifuka ke nema ruwa a jallo kan yakin Darfur, ya ayyana goyon bayansa ga zababben shugaban Amirka Donald Trump, tare da bayyana shi da kasancewa mai saukin kai.
Ya ce Trump zai fi mayar da hankalinsa kan abin da Amirkawa ke so, sabanin yadda wasu da ke ikirarin demokaradiyya da kare hakkin jama'a da gaskiya.
A hirar da jaridar Emirati al-Khaleej ta yi da shi, Al-Bashir ya ce sabon shugaban na Amirka dan kasuwa ne, wanda bashi da munafurci, face aiwatar da abunda abokan huldarsa ke muradi.
Kotun hukunta masu manyan laifuka ta ICC na zargin shugaban na Sudan da kisan kiyashi da aka yi a lardin Darfur da ke yammacin kasar.