Al Bashir ya kafa kwamitin bincike
January 1, 2019Talla
Shugaba al Bashir ya bukaci ministan shari'ar kasar Mohammad Ahmad Salem da ya jagoranci kwamitin binciken, sai dai bai fayyace takaimaimen abin da za a bincika ba.
Matakin na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da kasashen Amirka da Birtaniya da ma kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka yi na a bincika amfani da makaman da jami'an tsaro suka yi da suka kai ga kisan wasu.
Zanga-zangar da aka fara da batun tsadar rayuwa, ta rikide ta koma neman murabus din Shugaba al Bashir, wanda ya yi shekaru 29 yana mulki a Sudan.