Sudan na son sasantawa da kasashen yamma
June 2, 2015Talla
Wannan mataki dai da Bashir ya sha alwashin dauka na zaman wani sabon abu a kasar da ta kwashe tsahon shekaru a karkashin takunkumin karya tattalin arziki daga al'ummomin kasa da kasa. Bashir ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a gaban majalisar dokokin kasar jim kadan bayan sake rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar ta Sudan, inda ya jaddada cewa ya dauki wannan kudirin ne da zuciya daya domin ganin dangantakar da ke tsakanin kasarsa da sauran kasashen yamma ta koma dai-dai. Tun dai a shekara ta 1989 ne Shugaba Omar Hassan al-Bashir ke kan karagar mulkin shugabancin Sudan bayan da ya jagorancin juyin mulki a kasar.