Al-Bashir zai yi zaman kaso na shekaru 2
December 14, 2019Talla
A wannan Asabar din ce kotun ta yi zaman ta inda ta yanke wannan hukunci na zaman gidan maza na shekaru biyu saboda samun tsohon shugaban Sudan din da ta ce ta yi da laifi na cin hanci da karbar rashawa, musammun dangane da wasu kudaden da Saudiyya ta bai wa Sudan kusan Euro miliyan 81 wanda Al-Bashir din ya karkata akalarsu.
Wannan hukunci da kotun ta ta yanke, shi ne na farko daga cikin jerin hukunce-hukuncen shari'ar da ake yi al-Bashir din tun bayan da sojojin suka kifar da mulkinsa a cikin watan Afrilu da ya gabata sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa da jama'a suka yi bayan ya kwashe shekaru 30 a kan karagar mulki.