Allurar corona ga masu kula da aikin Hajji
March 26, 2021Talla
Ma'aikatar kula da ayyukan Hajji da Umrah a kasar Saidiyya sun ce sabuwar dokar ta shafi shaguna da kuma wasu karin ma'aikata da ke gudanar da ayyuka na musamman. Dokar rigakafin corona za ta fara aiki ne daga farkon fara azumin watan Ramadan da ake sa ran farawa a ranar 13 ga watan Afrilu, ko da yake har ya zuwa yanzu kasar ba ta fidda adadin wadanda za ta amince su gudanar da aikin Hajjin bana ba.
A farkon wannan watan ne dai ministan lafiyan kasar Saudiyya ya ce allurar rigakafin corona ta wajabta ga dukkan maniyatan aikin Hajjin bana. Tun farkon bullar annobar corona dai, gwamnatin kasar ta dauki matakin dakatar da ayyukan Umrah na dan wani lokacin tare da bai wa tsiraru 'yan kasar damar gudanar da aikin Hajji.