1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar:Ruwan sama sun kashe mutum 33

Abdourahamane Hassane
August 13, 2020

Gwamnati a Jamhuriyar Nijar ta ce ruwan saman da ake ci gaba da yi kamar da bakin kwarya tun daga watan Yuni har ya zuwa yanzu, sun yi sandiyyar mutuwar mutane 33 kana  suka raba wasu dubu 80 da  matsugunansu.

https://p.dw.com/p/3gvlP
Niger Überschwemmungen in Niamey
Hoto: DW/A. Mamane

Sama da gidaje dubu tara suka rushe a sakamakon ruwan ,da a  wasu yankunan a cikin shekaru 40 ba a taba samun saukar daminar kamar haka ba. Jihohin da suka fi shafuwa sun hada da Maradi da Tahoua da Tillaberi da Dosso da ke a yankin yammacin kasa. Domin kawo dauki ga wadanda lamarin ya rutsa da su gwamnatin ta fara rarraba  kayan abinci da sabulun wanka da tufafi da barkuna rufa ga jama'ar.