1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwan sama na barana a Afirka

Binta Aliyu Zurmi
September 11, 2020

Ambaliyar ruwan sama da ake ci gaba da samu a kasashe Afirka ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari biyu yayin da ya raba wasu akalla mutum miliyan guda da matsugunnansu a kasashen Senegal da Sudan.

https://p.dw.com/p/3iMLK
Überschwemmung in Nigeria
Hoto: picture alliance/dpa

Ofishin da ke kula da ayyukan jin kai na MDD na ganin a wannan shekarar bukatar agajin gagawa zai rubanya na shekarar da ta gabata a sabili da yadda ruwan ke ci gaba da yin barna. 

Kasashe goma sha daya ne ke fama da ambaliya a kasashen yammacin Afirka da ma kasashen taskiyar nahiyar ciki kuwa harda Najeriya da Nijar. 

Firai Ministan kasar Nijar Brigi Rafini a wata ganawa da ya yi da kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen ketare da wasu jakadun kasashen waje ya nemi a taimaka wa Nijar kasancewar girman barnar a kasar. Mutum saba'in da daya ne suka mutu yayin da ambaliyar ta shafi mutane dubu dari uku da hamsin.