1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa a kasashen Afirka ta Yamma

July 18, 2022

Ruwan sama mai karfi ya haddasa ambaliya a jihohin Najeriya da Nijar inda ta raba al'ummomi da gidaje da ma datse wasu muhimman hanyoyin da suka hada shiyyoyi da wasu jihohi na kasashen.

https://p.dw.com/p/4EIzH
Katsina Flut Nigeria
Hoto: DW/Y. Ibrahim

Sanadiyyar ruwan sama babu kakkautawa da aka yi a karshen mako a jihohin Borno da Yobe; da aka shafe awowi sama da 24 ana yi, an samu ambaliyar ruwa da ta rusa gidaje da lalata gonaki da dama. A karamar hukumar Gulani ta jihar Yobe akwai garuruwan da ambaliyar ta shafe kwata-kwata. Sun kuma hada ne da Bulunkutu da Bumsa da ke karamar hukumar Gulani a jihar Yobe inda dubban mutane suka rasa matsugunsu da dukiyoyinsu gami da abinci da ma dabbobi.

Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu labarin samun ko matsalar ta safi yarukan mutane ba. Haka ma ambaliyar ta raba hanyar Bauchi zuwa Gombe a wurare biyu abin da ya tilasta wa matafiya daga jihohin Gombe da Taraba da Adamawa yin zagaye mai nisa kafin su iya zuwa wasu sassan jihohin kasar.

Malam Musa Muhammad Gidado shi ne shugaban kungiyar ma'aitakan motoci da samar da ayyukan yi reshen jihar Gombe, ya kuma yi bayanin yadda ambaliyar ta datse hanyar da ke da muhimmanci ga al'umma shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Überschwemmung in Nigeria
Wasu daga cikin yankunan da ambaliya ta yi wa ta'adi a arewacin NajeriyaHoto: picture alliance/dpa

Malam Musa Muhammad Gidado, ya ce; ‘‘Direbobinmu na cikin wani hali da ma su motocin duka, saboda kwata-kwata ma aikin bai yiwuwa. Direba zai zo Tasha ya koma gida bai tafi ba fasinja ba. Yana cikin mawuyacin hali motocin ga su nan su lalace saboda wannan lalacewar da hanya ta yi a tsakanin Gombe da Bauchi.”

Hukumomi masu kai agajin gaggawa ga wadanda ibtila'i ke shafa sun kai dauki ga wadanda ambaliyar ta shafa da nufin saukake musu irin radadin da suke fama da shi tare da daukar matakai na magance sake faruwar ambaliyar ruwan a cewar su.

Malam Mamman Muhammad, shi ne daraktan kula da harkokin yada labarai na gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya kuma ce akwai matakan da gwamnatin jihar ta Yobe musamman ta dauka a kan wannan ibtila'i.

Ya zuwa yanzu dai ana kyautata zaton hukumomi na shirin gyara hanyar Gombe zuwa Bauchi duk da cewa akwai masu kasadar goya mutane a baya suna tsallakar da su zuwa bakin daya gabar ana biyan musamman ga mutane da garuruwansu ke kusa da inda hanyoyin suka lalace.