1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Yankin kudancin Afirka ya fuskaci bala'in ambaliyar ruwa

Ahmed Salisu SB
March 19, 2019

Iska mai karfi hade da ambaliyar ruwan sun janyo rasuwar mutane a yankin kudancin Afirka musamman kasashen Muzambik da Zimbabuwe da Malawi. Tuni dai masu ba da agajin gaggawa da kungiyoyin jinkai suka fara kai dauki.

https://p.dw.com/p/3FIXp
Mosambik Unwetter Zyklon Idai
Hoto: Getty Images/AFP/A. Barbier

Wannan dai shi ne karon farko da kasashen na kudancin Afirka suka gamu da matsala irin wannan wadda ta girgiza kasashen. Jami'an Majalisar Dinkin Duniya musamman ma wadanda ke aiki da shirin abinci na majalisar sun ce kimanin mutane milyan guda da rabi ne ke cikin hali na tsaka mai wuya a kasashen sai dai kasar Muzambik dai na kan gaba wajen yawan wanda wannan Ibtila'i na guguwa da ambaliyar ruwa suka fi shafa.

Simbabwe, Chimanimani: Spuren des Zyklons Idai
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ta tabbbatar da rasuwar mutane 84 a hukumance amma kuma shugaban kasar Filipe Nyusi ya ce bisa ga abin da idonsa ya gane masa akwai yiwuwar yawan mjutanen da suka rasu ya karu sannan jama'a da dama a halin yanzu na cikin mawuyacin hali.

Galibin wandanda lamarin ya shafa dai suka ce cikin dare ne suka ankara bayan da ruwa ya fara cika gidajensu kafin kuma daga bisani iska mai karfin gaske ta fara yaye rufin matsugunansu. Wata budurwa 'yar shekaru 14 da abin ya shafa ta ce abincinsu da kayan karatunta duk sun salwanta sakamakon wannan matsala da kasar tasu ta Muzambik ta fuskanta.

Mosambik Unwetter Zyklon Idai
Hoto: Getty Images/AFP/A. Barbier

Yanzu haka dai kungiyoyin ba da agaji na kasa da kasa na ci gaba da kokari wajen ganin sun bada tallafi ga yankin da lamarin ya shafa musammann ma dai birnin na Beira inda kashi 90 cikin 100 na gidajen birnin suka rushe yayin da saura suka cika da ruwa.

A share guda kuma masana hasashen yanayi na cewar akwai yiwuwar sake fuskantar ambaliyar ruwa, lamarin da ya sanya ake kiraye-kiraye ga sauran kasashe da su tashi haikan wajen ganin an tallafawa Muzambik da sauran kasashen da abin ya shafa da nufin ceto sauran wadanda ke da sauran shan ruwa a gaba.