Amfani da kafofin sadarwa wajan tallace-tallace
February 24, 2016Shi dai Kader Mai dalili, wani matshi ne dan shekaru 38 a duniya, wanda ya maida hankali ga amfani da kafofin sadarwa na zamani irin su Whatsapp, Facebook ko Twitter, ta hanyar tallata wa masu ayyukan hannu kayayyakinsu musamman matasa da su ka guji zaman kashe wando domin basu kwarin gwiwa.
Hashimu Ada shima wani matshin ne da ke kanikancin babur wanda kuma ya ci moriyar tallar da Kader Mai dalili ya yi masa ta wadan nan hanyoyi inda shima ya nuna gamsuwar sa da wannan tsari. Kader Mai dalili dai ya nada kimanin wasu matasa guda ukku da ya ba wa horo ga wannan sabuwar fusa'ar.
Yanzu haka wannan husa'ar ta Kader Mai dalili, ta samu karbuwa ga jama'a musamman ma'abuta kafogin sadarwa na zamani kamar yadda Sahabi Abbas, wanda ya hadu da wani magyarin na'urar sanyaya ruwa ta wannan hanyar ya kuma yaba yadda kafofin sadarwa na zamani ke taka rawar gani ga rayuwar al'umma ta yau da kullum