Amfani da lambu wajen yaki da hamada
Yankin Sahel na Afirka na daga cikin yankunan da suka fi bushewa a duniya. Daruruwan lambuna ne ke samuwa yanzu a Senegal, cikin shirin kare muhalli na "Green Wall," da kuma ke iya samar da abinci.
Dashen bishiyoyi na 'Green Wall'
A shekarar 2007 ne aka kaddamar da shirin dashen bishiyoyi da aka sanya wa suna 'Green Wall.' Manufar hakan shi ne domin maganta matsalar hamada a yankin Sahel. Shiri ne na shuka bishiyoyi na tazarar kilomita 8,000 daga kasar Senegal zuwa Djibouti. Amma aikin na tafiyar hawainiya, inda kashi 4% ne na hekta miliyan 100 da aka yi alkawari ne kacal aka yi shukar a kai kawo yanzu.
Senegal: Lambu maimakon dashen bishiyoyi
Senegal ta bullo da wata dabarar kare muhalli da za ta maye shirin Green Wall: Yanzu za a kafa daruruwan lambuna a kasar. Ana kiran shirin "Tolou Keur" a harshen kasar, Wolof, inda ake shuke-shuken da ke iya jure wa zafi da busasshen yanayi. Tsarin kunyar noma da ake iya gani a wanna hoto na taimaka wa kasa ta iya rike ruwa ko danshi.
Bishiya daya, mataki ne na amfanin shekaru
"Idan ka shuka bishiya daya, mutane da dabbobi za su ci amfaninta na fiye da shekaru 20." a cewar Moussa Kamara, daya daga cikin masu aikin kafa lambu. Asalin sa mai aikin gasa burodi ne, sai dai kamar sauran mutane da dama a yankin, yana taimakawa wajen shuka kayayyaki domin samar da lambu da zai taimaka wajen bai wa muhalli kariya.
Matakin kare shuka saboda samun abinci
Wannan shiri na taimaka wa mazauna karkara zama masu dogaro da kansu. Misali suna dasa bishiyoyin mangoro da gwanda ko kuma zogale a lambu, suna samun kudade. Shuke-shuken na kuma samun kariya daga barazanar iska ko guguwa da ma dabbobi. Ana iya samun haka ne idan aka yi wa shuka rufi kamar wanda ake iya gani a wannan karamar bishiyar lemon tsami da ke Walade.
Wasu daga cikin matsaloli...
Kauyen Walade, guda ne daga cikin yankunan da aikin kula da lambu ke da wuya. Akwai matsalar rashin samun injunan ban-ruwa masu amfani da hasken rana. Sannan, hamada na ci gaba da cinye yankuna. Sai dai duk da hakan, nan ma mutane na aikin shuka bishiyoyin babu kama hannun yaro, domin kare matsalar kwararowar hamadar.
...sai kuma nasarori
A gabashin yankin Kanel ga misali, lambunan na habaka. A nan mutane sun shawo kan rashin famfunan ban-ruwa ta hanyar tsara magudanun ruwa cikin shuka irin na rani. Yanzu akwai akwai gomman lambuna a Senegal, watanni bakwai da fara wannan aiki. Akwai daruruwa kuma da ke tafe.