Sabuwar mai shari'a ta kotun kolin Amirka
October 27, 2020Talla
'Yan jam'iyyar Demokrats a majalisar sun nuna adawa da nadin wanda ya zo 'yan kwanaki kafin zaben kasar yayin da a nasu bangaren 'yan Republican suka barke da tafi bayan da aka tabbatar da ita.
Wakilai 52 suka kada kuri'ar amincewa da nadin yayin da 48 kuma suka kada akasin haka. Shugaban Amirka Donald Trump ya baiyana gamsuwarsa inda yace majalisar ta yi abin da ya dace.