Amirka: Batun birnin Kudus ya kusa
February 23, 2018Talla
Gwamnatin Amirka ta ce tana sa ran cikin watan Mayun bana, za ta kaddamar da ofishin jakandancinta a birnin Kudus na Isra'ila, bayan ayyana birnin a matsayin fadar gwamnatin Isra'ilar da shugaba Donald Trump ya yi bara. Bude ofishin na Amirka a birnin na Kudus zai yi katari ne da kafuwar Isra'ila shekaru 70 a cewar wani babban jami'in Amirka da bai so a bayyana sunansa ba.
Ayyana wannan birni a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila da Mr. Donald Trump ya yi a bara, ya fusata hatta kasashen Larabawan da ke kawance da Amirka ganin yadda Falasdinawa ke son bangaren birnin ya kasance fadarsu. Tuni ma dai ministan ma'aikatar tattara bayanan sirrin Isra'ila, wato Mr. Israel Katz ya yaba shirin Amirkar na kaddamar da ofishin nata a birnin na Kudus.