SiyasaArewacin Amurka
Amirka: Bore ya lakume Dala biliyan biyu
September 1, 2020Talla
Daraktan Kula da Ayyuka a birnin Shelly Billingsley ya ce masu zanga-zanga sun yi ta'adi sosai a kan kayan gwamnati, biyo bayan harbin Blake din da aka yi a watan da ya gabata. Wannan na zuwa ne a yayin da ake zullumin barkewar tashin hankali a birnin na Kenosha gabanin ziyarar da Shugaba Donald Trump ya shirya kai wa birnin a wannan Talata.