1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Amirkawa za su salwanta a makon gobe

April 5, 2020

Babban  Jami'in Kula da Kiwon Lafiya na Amirka Jerome Adams ya ce Amirkawa su shirya, makon da za a shiga zai kasance mai tsauri kuma mara dadin ji, da dadin gani.

https://p.dw.com/p/3aU4V
USA Präsident Donald Trump Coronavirus Pressekonferenz
Hoto: Reuters/J. Roberts

Jerome Adams  ya ce abubuwan da kasar za ta shaida daga annobar coronavirus za su kasance tamkar na harin kunar-bakin waken da aka kai mata na ranar 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001.

Likitan ya yi hasashen cewa a wannan mako da za a shiga, Coronavirus za ta kashe Amirkawa kuma ba wai a jiha guda daya kawai ba, za a samu rasa rayuka a dukkanin sassan kasar.

Kawo yanzu dai Amirka na da mutane sama da 312,000 da suka kamu da Coronavirus, kuma cutar ta kashe akalla mutum 8,500.