1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Turai sun hana jiragensu zuwa Isra'ila

July 23, 2014

Hukumar da ke kula da al'amuran zirga-zirga na jiragen sama ta nahiyar Turai AESA,da ta Amirka FAA sun dakatar da zuwan jiragensu a Isra'ila

https://p.dw.com/p/1CgvF
Flugzeug EL AL
Hoto: JACK GUEZ/AFP/Getty Images

Jami'an hukumar sun dakatar da zirga-zirga na saukar jiragensu a filin saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke a Tel Aviv har sai abin da hali ya yi. Tun farko hukumar kula da al'amuran tashin jiragen sama ta Amirka ta FAA ita ce ta yi haramci ga kamfanonin ƙasar na tsawon sao'i 24.

Bayan da wani makami na roka da aka harba daga Gaza ya faɗa a kusa da filin jirgin saman na Tel Aviv. Wannan shi ne karo na farko tun bayan yaƙin Golf a shekarun 1990 da irin wannan haramci ya shafi Isra'ila.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usmanm Shehu Usman