Amirka ta soke cinikin makamai da Saudiyya
July 18, 2019Talla
'Yan majalisar dokokin na Amirka sun dauki wannan mataki ne a sakamakon kisan gillar da jami'an gwamnatin Saudiyyar suka yi wa shahararren dan jaridar nan na kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi a kasar Turkiyya da kuma rawar da Saudiyyar ke takawa a yakin kasar Yemen.
Dama dai a watan Yunin da ya gabata wannan kudirin sayar da wadannan makamai ya bi ta gaban majalisar dattawan kasar ta Amirka wadda 'yan jam'iyyar Republican ke da rinjaye a cikinta. A nan gaba kuma zai isa a fadar White House.
Sai dai kuma Shugaba Donald Trump na da hurumin bijire wa wannan mataki na 'yan majalisar ta hanyar hawa kujerar naki da doka ta ba shi.