Kamala Harris za ta goya wa Biden Baya
August 12, 2020Talla
Kamala Harris dai ta kafa tarihin zama mace bakar fata ta farko da ta taba samun damar tsayawa a matsayin abokiyar takarar shugaban kasa a tarihin Amirka.
Harris mai shekaru 55 da haihuwa kuma yar asalin Indiya da Jamaica da ke wakiltar jihar Carlifonia na zama guda daga cikin mata kusoshin jam'iyyar Democrats.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Biden ya ce yana cike da alfahari da wannan zabin na Harris a matsayin mataimakiyarsa, inda ya ke bayyana ta a matsayin ma'aikaciyar gwamnati mafi inganci a kasar.
A wannan Laraba za su yi fitar farko a matsayin abokan takara da ke shirin fafata wa da shugaba mai ci Donald Trump.