Amirka: Mun kashe shugaban IS a Afghanistan
July 15, 2017Talla
Cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar tsaron Amirka Dana White ta fitar, ta ce harin da sojojinta suka kai a ranar 11 ga watan Yuli ne ya yi sanadiyyar mutuwar Abou Sayed da wasu membobin kungiyar el-Khorasan. Ita dai kasar Amirka ta rubanya matakan yaki da masu kaifin kishin Islama a Afghanistan, saboda tsoron kada kasar ta zama sabon dandali na jihadi, kamar Iraki da Siriya.
Abu Sayed ya zama shugaban masu kaifin kishin Islama na uKu da sojojin Afghanistan da Amirka suka kashe bayan Hafiz Sayed Khan a bara da kuma Abdul Hasib a watan Afrilun 2017. Dakarun Afghanistan da kuma na Amirka sun kaddamar da wani farmakin hadin gwiwa tun a watan Maris shekara ta 2017 da nufin ganain bayan mayakan sa kai a Afghanistan.